Image

image

Advertisements

65 Reasons to Believe Jesus Did Not Die on the Cross

This post was originally made by Ghulam Ahmed Rabbi Author: Imam I. H. Kauser, National President of Ahmadiyya Muslim Community, Australia Click to Watch Video: Govt. of India Documentary on Jesus…

Source: 65 Reasons to Believe Jesus Did Not Die on the Cross

ILLAR YADA ALFASHA A TSAKANIN AL’UMA

   A gaskiya musulunci bai koyar damu irin wannan ta’assubanciba, ya kamata ADMIN na zaurukan (group-group) da muke dasu a facebook da saura shafukan internet sukula da masu qoqarin yada fasadi da rarrabuwar kawuna tsakanin musulmi. Tahanyar yada qarya,qage kalaman 6atanci domin hanasu cimma wan an mummuna aiki (nufi) nasu, domain gujewa tarayya acikin aikin 6arna.
قال تعالي:
“ﺇﻥ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺤﺒﻮﻥ ﺃﻥ ﺗﺸﻴﻊ ﺍﻟﻔﺎﺣﺸﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻟﻬﻢ
ﻋﺬﺍﺏ ﺃﻟﻴﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﺍﻵﺧﺮﺓ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻳﻌﻠﻢ ﻭﺃﻧﺘﻢ ﻻ ﺗﻌﻠﻤﻮﻥ”
وروا ﺍﻹمام احمد
ﻋﻦ ﺛﻮﺑﺎﻥ ، ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ” ﻻ
ﺗﺆﺫﻭﺍ ﻋﺒﺎﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺗﻌﻴﺮﻭﻫﻢ ، ﻭﻻ ﺗﻄﻠﺒﻮﺍ ﻋﻮﺭﺍﺗﻬﻢ ، ﻓﺈﻧﻪ ﻣﻦ ﻃﻠﺐ ﻋﻮﺭﺓ ﺃﺧﻴﻪ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ، ﻃﻠﺐ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻮﺭﺗﻪ ، ﺣﺘﻰ ﻳﻔﻀﺤﻪ ﻓﻲ ﺑﻴﺘﻪ ”
Allah mai girma da daukaka yana cewa:- “Lallaine wayannan da suke shawar yada alfasha (ayukkan barna) tsakanin masu Imani ( al’umar musulmi) Allah ya la’ane a (cikin) rayuwar duniya da lahira kuma suna da azaba mai radadi (tsananin quna)”
Daga Thaubana yace:- Manzon Allah tsira da amincin Allah sutabbata gareshi da iyalansa yace:”Karku (al’umar muslmi) cutar da bayin Allah,kada ku aibantasu kuma kada kunemi sanin al-aurarsu (bincikar sanin abin da suka 6oye na sirrinsu da basuso a saniba). Domin kuwa duk wanda ya nemi tona (cinmutuncin/tozarta) asirin musulmi,lallai Allah zai tona (tozartashi) asirinsa duniya da lahira”. Imamu Ahmad ya ruwaici hadithin.