Gyara kanka

MUSLUMI MU GYARA KAFIN ALLAH YA GYARA
MANA
Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Dukkan yabo da
godiya su tabbata ga fiyayyen halitta Manzon
Allah Muhammadu dan Abdullahi tsira da aminci
su tabbata gareshi da iyalanSa har zuwa ranar
dukiya da ‘ya ‘ya basa amfanar mutum da komai
saifa ga wanda ya zowa Allah da zuciya mai
tsarki. ‘yan uwa musulmi na zabi na yima wannan
maqala tawa take da MUSLUMI MU GYARA KAFIN
ALLAH YA GYARA MANA. Lalaine ga duk wani
musulmin Nigeria da ke da shekaru irin nawa a
birni yake ko a kauye bai jahilci cewar yanzu
musulmin Nigeria yana cikin halin kunci, zilla da
rashin tabbatacciyar makoma saboda abinda
hannuwanmu suka aikata ko suke kan aikatawa,
imma tsakanin junanmu (musulmi) ko kuwa da
abokan zamanmu mabiya sauran addinai
masamman (kiristoci). Shi dan Adam da Allah ya
halicceshi bai yishi hakanan ba qaidi (wato batsari
da iyakoki) ba hasalima dashi wannan tsarin Allah
ya bambantamu da dabbobi, a cikin wannan tsarin
ne Allah ya sayan mizamin saninSa tahanyar aiko
Manzani alaihimussalam da cikakken sako, ya
sanya bin sakon a matsayin ibada (addini), sai
yazama kammaluwar mutum zuwa cikar mutum-
takasa tana danfare ne ga biyyarsa ga wannan
tsarni (wato ga bin dokoki/tsare-tsaren addini),
har yazamo shi mutum rayuwar dukkanta addini
ce, kama daga kasuwancinSa, Aurensa, gudanar
mulkinsa, huldarsa ( da mutune, dabbobi da abinda
da ke zagayensa na sauran halittu). Allah mai
Tsarki yace:- “BABU WANI ABU (na daga rayuwar
dan Adam) FACE MUNYI BAYANINSA ACIKIN
LITTAFI ( wato Alqur’ani)”. Lallaine, manzon Allah
yazo da alqur’ani a matsayin hanya shiriya ga
dukkanin al’umma har izuwa ranar qiyama. Ya
zama shi wannan Alqur’ani ya share dukkan wata
doka (Littafai/takardu ko tsarin rayuwa) ta
Annabawa da al’ummun da suka shude. Alqur’ani
ya fadamana cawer:-…INA MAIYI MAKU BUSHARA
DA MANZON NAN DA ZAI ZO ABAYANA SUNANSA
AHMAD YAYIN DA YAZO MUSU DA BAYANI
(Alqu’ani) SAI SUKACE AI WANNAN SIHIRINE
BAYYANANNE, haka kuma hadisi yazo daga bakin
Sadiqul Amin (S A W) yana cewa:-“ NINE
KARSHEN ANNABAWAN DA BA ANNABI BAYANA”
Manzon Allah kamar sauran Annabawa ya kirayi
mutane zuwa biyar tsari tsaftatacce (Musulunci)
“….BABANKU IBRAHIMA SHINE WANDA YA
AMBACEKU MUSULMI TUNFARKO”. Muslunci kuma
addini ne mai cike da hikimomi da tsari
ingantacce,waje kiran mutane ( masamman
wayanda ba musulmiba) zuwa ga bautar Allah da
tausaya musu a cikin mu’amala da wasu al’amurra
rayuwa Allah yana cewa a cikin mabuwayin
littafinSa :-“….. DA DAI KA KASANCE (ya Manzon
Allah) MAI KAUSHIN ZUCIYA DA SUN WATSE DAGA
BAYANKA (wato sun gujeka)”, Mai tsira da Amincin
Allah sutabbata agareshi yace;- “an aikoni (da
manzanci) ne domin incika kyawawan dabia”.
Amma abin kaico ! , dukkan dabi’un da musulunci
ya gina al’umar Annabi dasu yau akasinsu shi mu
(al’umar musulmi) ke aikatawa. Mun koma ba
Amana tsakaninmu, shuwagabanninmu da masu
kudinmu basa adalci ga mabiyansu, manyanmu
basa tausayin kanananmu, su kuwa kananan basa
girmama manyanmu, babu kunya ga
matanmu,mafi yawan masana addinin(malaman)
cikinmu kansu a waste yake, neman girma da son
duniya shi suka sa gaba” ……..KOWACE KUNGIYA
DA ABINDA KEGARETA TAKE (ALFAHARI)
TAKAMA” .Alhali MaiGirma da Daukaka yana
fada :- “….IDAN KUKAYI JAYAYYA, KUKA RARRABA
KARFINKU ZAI TAFI”. Acikin wannan mummunan
yanayi sai kuma yakasance Jahilai da Talakawan
cikinmu sai girman kai, kwadayi da rashin qana’a
ya yawaita tsakanin almajiran cikinmu, sai
yazamana al’umar musulmi batada mai kwabarta a
cgkin umurni da hani. Sai yazama sauran al’ummu
suna dada qarfi da dunkulewa wuri daya ita kuma
al’umar musulmi tana dada rarraba, har takai ‘yan
ta’adda da qungiyoyin ‘yanfashi suna amfani da
sunan musulunci wajen qara shafawa musulmi da
musulunci kashin kaji.
Da wannan nake ganin yadace Musulmi mu aje son
rai mu komama Allah da tuba, mu riqe amanonin
da Allah ya dora mana ko masamu canjin rayuwar
mu. Domin ko lalai musulmi muna cikin qunci da
zilla saboda abinda hannu wanmu take kan
aikatawa

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s